Labarai

Hisbah Ta Bawa ‘Yan Jaridu Gurbin Mutane 50

AUREN ZAWARAWA: Hisbah Ta Bawa ‘Yan Jaridu Gurbin Mutane 50

Hukumar Hisbah ta jihar Kano tace zata sanya ‘yan jarida 50 a Auren Gata da gwamnatin Kano ke yi.

Shugaban hukumar Sheíkh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan yayi wata ganawa da manema labarai.

Daurawa yace za su bada dama ga ‘yan jarida 50 dake Kano ko kuma masu aiki a kafafen yaɗa labarai dake da sha’awar shiga tsarin auren gata da gwamnatin Kano take gudanarwa domin cin gajiyar shirin.

“Haka kuma, zamu bada dama ga Malaman addini, Ma’aikatan lafiya dake son shiga tsarin na auren gata wanda a baya mutane sama da dubu ɗaya suka amfana da shirin.” Inji shi

 

Back to top button
error: Content is protected !!