Labarai

Cire Haraji Domin Tsaron Yanar Gizo Abu Ne Mai Muhimmanci

Cire Haraji Domin Tsaron Yanar Gizo Abu Ne Mai Muhimmanci – Cewar Ƙungiyar Tabbatar Da Cigaban Najeriya.

Gamayyar ƙungiyoyi fafutuka kan cigaban Najeriya, “Nigeria First Project” (NF-PRO) sun bayyana cewa tsarin cirar haraji domin gudanar da tsaron yanar gizo ba wani abu ne da zai zama illa ga ƴan ƙasa ba.

A ranar 6 ga watan Mayu, 2024 babban bankin Majeriya, (CBN ya umarci bankuna da sauran hukumomin hada-hadar kuɗi da su aiwatar da tsarin cirar kaso 0.5 daga kuɗaɗen hada-hada domin gudanar da tsaron yanar gizo-gizo.

Mahukunta sun bayyana cewa tsarin zai fara aiki cikin makonni biyu sannan kuma abin da aka cira kaitsaye zai na shiga asusun ƙasa na kula da tsaron yanar gizo wanda ke ƙarƙashin Ofishin mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

Ƴan Najeriya da dama sun koka game da tsarin inda mutane daban-daban ke kiraye-kirayen a dakatar da shi ciki har da wasu ƴan majalissar wakilai.

Da yake gabatar da jawabi cikin taron manema labarai da suka kira a Kano, shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Hamza Saulawa ya bayyana cewa manufar cire harajin ita ce yaƙi da laifuffukan da ake aikatawa ta yanar gizo.

“Duba da yadda ake cigaba da samun ƙaruwar laifuffuka ta yanar gizo a Najeriya da kuma illar da hakan zai yi wa ƙasarmu muka fito mu nuna goyon bayanmu kan tsarin cirar haraji tare da duk wasu ƴan kishin ƙasa domin ganin kima da darajar ƙasarmu sun farfaɗo”. In ji Saulawa.

Ya kuma ƙara da cewa sun gamsu da bayanan da shugaban kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri na majalissar dattawa, Sanata Shehu Umar Buba yayi. Tare da neman ƴan Najeriya su ba da haɗin kai kan shirin su yi watsi da zantukan da wasu ke yaɗawa domin neman ɓata shirin.

“Yana da muhimmanci ƴan Najeriya su san cewa laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo ba tattalin arziƙin ƙasar kaɗai suke rusawa ba har ma da cigaba da ɓata ƙasar a Idon Duniya”. Ya ce.

“A yau, ƴan Najeriya da ba su da laifin komai Duniya tana yi musu kallon gurɓatattu, suna zama abin zargi a filayen jiragen sama da ofisoshin jakadancin ƙasashe da tashoshin mota”. In ji shi.

“Wani ƙarin abin tsoro a yau shi ne; matasa da dama a Najeriya sun shiga harkar damfara a yanar gizo domin su yi kuɗi cikin sauri. Wasu daga cikin waɗannan matasa gani suke zuwa makaranta ma cuta ce da ɓata lokaci kawai”.

“A yanzu muna da damar da za mu shawo kan wannan matsala. Abin mamaki akwai waɗanda suke ganin kaso 0.5 da za a na cirewa wasu kamfanoni da ma’aikatun hada-hadar kuɗi da aka tsara a jadawali na biyu na dokar tsaron yanar gizo ta shekarar 2024 yayi yawa. Amma kuma a gefe guda ba sa magana kan abubuwan da ake hasara ta fuskar tattalin arziƙi da zamantakewa sanadiyyar laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo”.

A cewarsu, tsana ko adawa da tsarin cirar harajin ba zai amfanar da kowa komai ba. “Daɗi da ƙari, mu ba mu ga aibun wannan doka ba kuma ba mu ga tayadda kuɗin yayi yawa ba, muna da cikakkiyar ƙwarin gwiwa a kan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Shehu Buba wanda ke zaman shugaban kamitin tsaro da tattara bayanan sirri na majalissar dattawa, ya bayyana cewa harajin yaƙi da laifuffukan yanar gizo ba ɗaiɗaikun ƴan Najeriya zai shafa ba ko kwastomomin banki ba.

Buba wanda ya ɗauki nauyin gabatar da ƙudirin yi wa dokar kwaskwarima, ya bayyana cewa tsarin zai shafi hukumomin hada-hadar kuɗi da kamfanonin sadarwa ne a matsayinsu na masu ruwa da tsaki.

Back to top button
error: Content is protected !!