Kannywood
Rizqat Sani Yar Gidan Sani Danja Da Zata Amarce
MashaAllah! Yarinyar Sani Danja Da Mansurah Isah (Rizqat) Zata Amarce! Ga Katin Gayyatar Auren Nata.
Babbar Yarinyar Jarumin Fina Finan Hausa Sani Danja Da Mansurah Isah, Wato Rizqat Sani Danja Zata Amarce. Inda Zata Aure Abdulsalam Abdulhameed,
Daurin Auren Da Za.ayishi A Ranar 18 Ga Watan Biyar Na Shekarar 2024, Za a Daura Auren Ne A Masallacin Jumma’a Na Unguwar Tudun Wada Dake Karamar Hukumar Nasarawa A Garin Kano.
Ubangiji Allah Ya Kaimu Lokacin Lafiya. Kuma Allah Ya Basu Zaman Lafiya, Amin.