Zahirin Abin Daya Faru Da Tsohuwar Jaruma Maryam Wazeery
Asalin Zahirin Abin Daya Faru Da Tsohuwar Jarumar KannyWood Maryam Wazeery Tare Da Mijinta Tsohon Dan Wasan Nigeria Tijjani Babangida. Da Iyalansu.
Tsohuwar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Musa Waziri wadda ke amsa sunan Laila Masu Gonar Naira a tsohon shirin Labarina Series da ya gabata, ta gamu da mummunar hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da mijinta, Tijjani Babangida wadda tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya ne, da d’an ta Muhammad Fadeel da kuma kanin mijinta, Ibrahim Babangida a ranar Alhamis.
Kanin mijinta, Ibrahim Babangida, shi ya ke tuka motar da su ke ciki lokacin da hatsarin ya faru, wadda kuma a take Allah Ya karbi rayuwar sa, in da aka garzaya da ita kuma Maryam da d’anta da mijinta zuwa Asibiti don kula da lafiyar su.
Sai dai kwana daya da hatsarin (wato a daren jiya kenan) Allah Ya yi wa karamin d’an na ta, Fadeel rasuwa shima sakamakon buguwar da ya yi.
A yanzu haka dai a cikin mutum 4 da su ka yi hatsarin, Maryam da mijinta ne su ka saura, in da su ke karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zariya.
Daga cikin abun da wannan hatsari ya jawowa tsohuwar tauraruwa Maryam Waziri shine mummunan raunin da ta ji a bangare daya na fuskar ta:
Ido
Kunne
Hanci
Dama bakin ta duka sun samu matsala.
Da fatan Allah Ya jikan Ibrahim da Fadeel, Ya gafarta musu. Ya bawa Maryam da Tijjani Babangida lafiya. Amin.
Daga Ahmad Nagudu