Kannywood

Ina Gargadi Ga Masu Amfani Da Sunana Suna Damfara

A’isha Humaira Tayi Kira Ga Masu Amfani Da Sunanta A Shafukan Sada Zumunta Suna Damfarar Mutane Da Su, Daina Ko Kuma Su Hadu A Gaban SHARI’A

Fitacciyar Jaruma a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood A’isha Humaira tayi kira tare da gargaɗi da jan kunne ga masu buɗe Account da Page a shafukan sadarwa na zamani da sunanta su daina in kuma sun ƙi to za ta gurfanar da su a gaban shari’a.

Humaira ta bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ta yi da Jaridar Dokin Ƙarfe TV, inda ta ƙara da cewa “Wasu na amfani da sunana suna aikewa mutane da Account Number na Opay da sunan a tura musu kuɗi. Wasu kuma suna ɗora bidiyo da hotunan da ba su kamata ba, tun a baya na yi gargaɗi kusan sau biyu an ƙi a daina. Yanzu a karo na uku ina fatan su daina tun da girma da arziƙi, ko mu haɗu da su a gaban kotu”. In ji ta.

Humaira ta kuma ƙara da cewa mutane su yi hattara su daina sakin jiki da duk wani Account mai ɗauke da sunanta in ba nata na asali ba dake a Instagram ko TikTok domin kuwa hatta a shafin Facebook ba ta da Account nata ko daya. “Yanzu haka hukuma suna cigaba da binciken waɗanda suke aikata wannan laifi, kuma duk waɗanda aka gano suna da hannu za su fuskanci shari’a”. A cewarta.

Back to top button
error: Content is protected !!