Kannywood

Idan Zango Ya Aureni Zai Sameni Da Budurcina

Idan Adam A Zango, Ya Aure Ni. Zai Sameni A Matsayin Budurwa Mai Dauke Da Budurcin Ta, Inji Wannan Matashiyar Aisha Shushu.

Wata jaruma a masana’antar Kannywood mai suna A’isha Shushu ta bayyana cewa tana matuƙar ƙaunar Adam A. Zango kuma ta amince ko gobe ne a ɗaura musu aure matuƙar ya amince yana sonta zai aure ta.

Aisha Shushu

Shushu ta bayyana haka ne ta cikin wata tattaunawa da tayi da Jaridar Dokin Ƙarfe TV, inda ta ce “Duk da kasancewa ta Jaruma a masana’antar Kannywood ni ɗaliba ce mai karatun Digiri a Jami’a, kuma har yau ina nan tare da budurcina, matuƙar Adamu ya aure ni to ina tabbatar masa cewa zai same ni ne a matsayin cikakkiyar mace wacce ba ta taɓa sanin wani ɗan namiji ba a rayuwarta”. A cewar ta.

A’isha ta kuma ƙara da cewa za ta zamewa Adamu mace tagari wacce za ta share masa hawayen da matan da ya taɓa aura suka haifar masa da zubarsu daga Idanunsa. “Zan tarairaye shi kamar ƙwai na share hawayen dake malala a Idanuwansa na yi rayuwa ta dindindin da shi”. In ji Shushu.

Back to top button
error: Content is protected !!