Kannywood

GasKiyar Magana Kan Halin Da Adam A Zango Ke Ciki

Wannan Itace GasKiyar Magana Kan Halin Da Jarumi Adam A Zango Ya Tsinci Kanshi A Halin Yanzu!

SHARHI: Bashir Abdullahi El-bash

Na bibiyi maganganun Adam A. Zango na kuma yi nazari game da halin da yake ciki a masana’antar Kannywood na fahimci cewa babu abin dake damun Adamu sama da matsalar rayuwa ta yau da kullum da kuma baƙin cikin rabuwa da matarsa ta ƙarshe wato Safiya Chalawa.

Magana ta gaskiya a iya fahimtata da nazari da bincikena waɗannan matsaloli biyu sune matsalar Adamu, kuma sune abubuwan da suka sa shi yin waɗannan maganganu masu kama da hannunka mai sanda.

Yayi maganar cewa hatta a cikin waƙoƙinsa yana bayyana matsalarsa amma abokan sana’arsa sun gaza fahimtarsa. Sannan ya ce ba sa shiga su tare masa faɗa ko su kare shi, (musamman waɗanda ya taimaka a baya). Jama’a duk waɗannan maganganu da Adamu yayi idan za mu nazarce su za mu iya cewa tallafi yake nema, yana neman gudunmawarsu ne a babin rayuwar yau da kullum. Ba wai kan rigima ba.

Duk wanda ya san Adamu a Kannywood zai tabbatar da cewa mutumin kirki ne wanda hannunsa a buɗe yake. Ya tallafawa mutane a lokacin da ludayinsa ke kan Dawo. Sai dai a yanzu rayuwar ta sauya tayadda za mu iya cewa a yanzu Naira 50,000 sha’awa za ta ba wa Adamu, kuɗin da ada bai fi ya sha alawa da shi ba. Ba wai ina nufin Adamu yana cikin matsanancin talauci ba ne, a’a, amma dai abin ba kamar da ba ne.

Ba Adamu kaɗai ba, duk mutumin da ya san daɗin kuɗi kuma ya zo ya rasa ba shakka zai shiga damuwa da zargin mutane musamman waɗanda ya taɓa taimakawa a rayuwa. Zai riƙa ganinsu ta fuskoki kala-kala kamar yadda Adamu ke ganinsu yanzu.

Dan haka ni a fahimtata da ganina babban gatan da ƴan Kannywood za su yi wa Adamu a yanzu shi ne su kafa ko da gidauniya ta musamman su haɗa masa wani abu mai ƙauri wanda zai kawai masa da damursa. Sannan kuma su sasanta tsakaninsa da matarsa ta ƙarshe Safiya Chalawa inda hali. Domin kuwa babu wata ƴa mace da Adamu ke so sama da ita a yanzu.

Yi wa Adamu waɗannan abubuwa a ƙalla guda biyu zai kawar masa da duk wata damuwa ya sanya shi cikin farin ciki da walwala. Sannan ita ma masana’antar ta kuɓuta daga zarge-zarge tunda ba ta taɓa yi masa haka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!