Kannywood

Bola Ahmed Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Saratu Gidado

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Ya Yi Alhinin Rasuwar Saratu Gidado

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika ta’aziyya ga iyalai da abokan aiki, kana da masoyan fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood, Saratu Gidado, wadda ta rasu a safiyar jiya Talata a Kano.

A Wata sanarwa da mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai Mr Ajuri Ngelale ya rattaba wa hannu, Shugaban ya bayyana rasuwar jarumar fim din mai shekaru 56 a matsayin wani babban rashi ba kawai ga masu jimantawa kadai ba, har ma da al’ummar kasar baki daya,.

Sanarwar ta kara da cewa baya da gibin da rasuwar Saratu za ta bari a masana’antar fimafimai da nishadi, haka ma ba za a taba mantawa da Irin gudunmuwar da jarumar ke bayarwa a harkokin jinkai da bayar da tallafi ga mabukata ba.

Shugaban ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Kano, da yan uwa, da ma duk wadanda rasuwar Marigayiya Saratu Gidado ta shafa tare da addu’ar Allah ya jikanta da Rahama.

Back to top button
error: Content is protected !!