Babu Laifin Shugaba Tinubu Wajen Tashin Kayayyaki
Shugaba Tinubu Bashi Da Laifi Wajen Hawau Hawau, KayayyaKi A Nigeria, Laifin Na Yan Kasuwa Ne.
DAGA Bashir Abdullahi El-bash
Tun lokacin da Dala ta hau ta kai har wajen Naira 1800 farashin kayayyakin abinci da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum suke tashin gwauron zaɓi a Najeriya.
Matsalar ta sanya ƴan Najeriya zargin gwamnati. Sai dai kuma, tun bayan lokacin da gwamnatin ta ɗauki matakan da suka haifar da ruguzowar Dalar talaka ya gaza ganin farashin kaya ya sauka kamar yadda yake hawa in ta tashi.
Yau Dala tana ƙasa da 1,000 amma ƴan kasuwa sun ƙi sauko da kayayyaki. Wannan ita ce babbar alamar dake tabbatarwa ƴan Najeriya cewa ƴan kasuwa ne matsalarsu. Dan haka gwamnati ta sauke nata nauyin tayi abin da ya dace dala ta faɗo, yanzu ƴan kasuwa ne za su yi nasu su sauko da farashin kayayyaki.