Labarai

Asalin Abin Daya Faru Tsakanin Umar Bush Da Ibrahim

Wannan Shine Hakikanin Abunda Ya Faru Tsakanin Umar Bush Sadiq Da Ibrahim.

Daga Jamila Ibrahim 

Umar Bush

Da farko kowa yasan Ibrahim ya fara dauko umar yana masa video yana taimaka masa da abinci da sauransu tunda dama shi umar yawo yakeyi a ungwa yara suna tsokanar sa , toh tunda Ibrahim ya fara masa video yawon yayi sauki aka fara duba kaishi asibitu duba lafiyarsa har natsuwa ya dan fara shigan umar , dalilin video da Ibrahim ke masa har ya fara samun daukaka.

Cikin azumi da aka gayyatosu Abuja wani dan social media dan Neman suna sai da ya matsa yanason ganinsu su gaisa ya baro kano ya biyosu Abuja kaman mutumin kirki , kuma gidan manya da aka gayyaci umar sai da ya bisu dan a dama dashi .

Da yaga sharholiyar da sukeyi kuma yaga yaran nata samun connection da manya , ya cewa Ibrahim ya dinga tayashi posting abun siyasa a page dinsa DA kuma videon sa , Ibrahim yace gaskiya page dinsa bana siyasa bane kuma bazai iya posting wasu video wanda bana umar ba , shine baice komai ba yaje gidan iyayen umar ya kulla sharri cewa Ibrahim baya nemawa umar lafiya kudi yake nema da dan uwansu kuma baya bashi , videon da yake yana dorawa biyan Ibrahim ake.

Ran yan uwansu ya baci sukace ai basusan abunda Ibrahim keyi da dan uwansu ba kenan , suka kira Ibrahim suka ci masa mutunci , kuma wlh Ibrahim ko page bashida shi bare ma ace Ana biyansa kudin sa content ..

Yanxu shi wanchan dan social median gani yake makudan kudi ake samu shima so yake yayi suna ya sami kudi shiyasa da zaije gidansu iyayen umar yace yazo ne ya taimakwa umar ya sami lafiya , kuma yaje da takardan fili wai ya siyawa umar , wanda za’a nemawa lafiya meye hadinsa da fili ? Inba cin hanci ya basu ba ?

Sun dauke umar da sunan samo masa lafiya , sun hada da sadiq sunje sunata content dasu suna dorawa a social media, har sunyi creating pages a tiktok da sunan umar dan suta samun kudi dashi.

Tambayata anan idan har sabida ya nema masa lafiya ya daukeshi meh yasa suke masa video , meh yasa suka dauki sadiq da basu shiri basu dau Ibrahim da sukafi sabawa da umar ba.

Kunga a nan harda sadiq aka hada baki akayi watsi da Ibrahim, a ganin sadiq duk abunda za’a dinga samu shi za’a bawa , tunda lokacin da umar ke hannun Ibrahim duk abunda aka bayar a account din Ibrahim ake sawa.

Mutane uku sunci amanar Ibrahim…

Da umar da ya yarda ya bisu ba tareda Ibrahim ba..

Da sadiq da ya amince akayi watsi da Ibrahim….

Da wannan dan social median dan Neman suna , sai da ya gama bibiyar su kaman na kirki kafin ya zagaya yaje yayi masa makarkashiya.

jama’a muji tsoron mutum , idan sadiq zai iya juyawa Ibrahim baya lallai mutum abun tsoro ne ..

Abunda suka Manta shine arzikin Ibrahim umar keci , suna ganin kaman shi umar ne Allah keta bawa daukaka , basusan idan babu Ibrahim abun nasu bazaiyi armashi ba.

iyayen umar sunga manyan mota kofan gida da takardan fili sun nuna basu san Ibrahim ba.

Toh ba komai Allah ya hada kowa da rabonsa , wanda yayi Mai kyau zai gani.

Back to top button
error: Content is protected !!