Kannywood
Yanzun Haka Anamin Barazana Akan Na Fadi GasKiya.
“Bazan janye kalamai na zargin M@ɗigo a makarantar firamare a Kano ba.
Yanzu haka ana barazana ga rayuwa ta don na fadi gaskiya, ina rokon hukuma ta bani kariya
~ Cewar jaruma Mansurah Isah
Jaruma Mansura Isah ta yi zargin ana yiwa rayuwarta barazana ne tun bayan da ta ki janye zargin da ta kwarmata na cewar wasu kananan yara na aikata badala a wata Makarantar Gwamnatin Kano.
Tuni dai Ma’aikatar Ilimi ta Kano da Hukumar Hisbah suka musanta zargin bayan binciken da suka gudanar, har ma suka nemi Mansura ta janye zargin da ta yi.
Amma Mansura ta ce tana kan bakanta har ma ta kalubalanci yadda binciken hukumomin ya kasance tana mai zargin akwai yar burum-burum a ciki.