Dalilin Da Yasa Nake Kokarin Hadewa Da Peter Obi
Abin da ya sa muke ƙoƙarin haɗewa da Peter Obi da sauran jam’iyyun siyasar ƙasar nan – Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, sun yi nisa wajen tattaunawa da sauran ‘yan adawa a fadin kasar domin ganin yadda za su kwace mulki a hannun jam’iyyar APC a nan gaba.
Atiku, wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar shugabancin kasa a zaben 2023, ya ce ganawarsa da Peter Obi, watau dan takarar jam’iyyar Labour na nufin su dunkule waje guda.
Ya ce, ” Ga duk wanda ya ke gani za a samu wani rikici tsakanina da Obi to babu abin da zai faru ko kadan, kuma mu a nan gaba kowa a dauko don ya yi takara in dai ya cancanta zamu goyi bayansa.”
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, ya ce,” Ai a baya na fada cewa idan jam’iyarmu zamu hadu ace a bar wa mutumin da ya fito daga Kudu maso Gabas zamu yar da.”
Shin kuna ganin cewa zasu iyà haɗa kai su haɗu waje ɗaya?