Labarai

Adadin Wadanda Aka Kon@ A Masallaci Ya Karu Zuwa 11

Adadin Wadanda Aka Kon@ A Masallaci Ya Karu Zuwa 11 — ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce adadin mutanen da suka rasa ransu a harin da wani matashi ya kai wa wasu masallata a wani masallaci da ke karamar hukumar Gezawa a Kano ya kai mutum 11.

An yi zargin cewa matashin ya watsa fetur a masallacin tare da cinna wuta, sannan kuma ya kulle ƙofar masallacin, tare da mutum kusan 40 a ciki.

Rahotonnin sun ce matashin ya kai harin ne sakamakon rigima kan rabon gado.

Tuni dai ‘yan sanda suka ce sun kama maharin mai shekara 38.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba lokacin da mutane ke gabatar da sallar Asuba a garin Larabar Abasawa da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.

‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya shaida musu cewa ya aikata hakan ne da nufin ƙon@ wasu ‘yan uwansa da ke cikin masallacin waɗanda rigimar rabon gado ta shiga tsakaninsu.

“Abin da ya faru ba shi da alaƙa da ta’addanci, rigima ce da ta faru sakamakon rikicin rabon gado,” in ji Baturen ‘yan sandan yankin, Umar Sanda.

 

Back to top button
error: Content is protected !!