Muhimman AyyuKan Da Shugaba Tinubu Ya Aiwatar
Muhimman AyyuKan Da Shugaba Tinubu Ya Aiwatar Guda 23!
A baya-bayannan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da wasu muhimman manyan ayyuka guda 23 domin kyautatawa da inganta rayuwar ƴan Najeriya kamar yadda jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito su kamar haka:
1. Ya amince a ba wa matasa kaso 30 cikin muƙaman gwamnatin tarayya a dama da su.
2. Ya amince a farfaɗo gami da inganta asusun ba wa matasa tallafin jarin dogaro da kai.
3. Sakamakon dokar da aka zartar a shekarar 2023, ya amince a saka Naira Biliyan 25 a asusun ba wa matasa jarin dogaro da kai, sannan kuma za a sake saka Naira Biliyan 25 daga asusun gina rayuwar matasa wanda aka ware a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024.
4. Ya amince a fidda Naira Biliyan 60 ƙarƙashin shirin tallafawa matasa kan harkokin noma da kasuwanci.
5. Ya amince a kafa kwamitin kotakwana kan tattalin arziƙi domin shawo kan matsalolin tattalin arziƙin Najeriya da inganta shi.
6. Ya amince an biya bashin Naira Biliyan 7 kan hada-hadar musayen kuɗaɗen ƙasashen waje.
7. Ya amince babban bankin Najeriya CBN ya biya Naira Miliyan 500 domin a sauya fasalin jari.
8. An tura ƙudirin doka kan sabunta fasalin albashi da alawus-alawus da sauran haƙƙoƙi na ma’aikatan shari’a ga zauren majalissar ƙasa.
9. A ƙoƙarin rage ɓarnata kuɗaɗen gwamnati, ya haramtawa jami’an gwamnati fita ƙasashen waje na tsawon wata uku.
10. Ya amince an ɗaga darajar kwalejin gwamnatin tarayya ta gyaran haƙori a zamanance dake garin Inugu zuwa cikakkiyar jami’ar nazarin harkokin kiwon lafiya gabaɗaya.
11. Ya amince an fara aikin titin da ya tashi daga Legas zuwa Kalaba mai tsawon kilomita 700, har ma an miƙa kashin farko na aiki mai tsawon kilomita 47.47 ga ɗan kwangila.
12. Ya amince an fara aiwatar da kashin farko na tsarin ba da kaya bashi ga ƴan Najeriya.
13. Ya ƙaddamar da tsarin baiɗaya na bunƙasa yawan kayan da ake samarwa da kuma harkokin kasuwanci a Najeriya.
14. Ya amince a kashe Naira Biliyan 25 kan ayyukan lafiya guda 8,800 domin magance matsalar mace-macen mata masu juna biyu gami da tabbatar da haihuwar jarirai cikin aminci a ƙasa gaba ɗaya.
15. An samu nasarar ceto kuɗaɗen zuba jari Dala Miliyan 600 daga kamfanin ayyuka na Danish domin gyarawa da ɗaga darajar tashoshin gaɓar ruwa a Najeriya gabaɗaya.
16. An samu nasarar ceto Dala Miliyan 250 daga GAVI Support domin inganta ayyukan lafiya a Najeriya.
17. Ya amince an tsara aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagiri domin bunƙasawa da faɗaɗa hanyoyin tattalin arziƙin ƙasa.
18. Ya amince da ƙarin albashin ma’aikatan gwamnati.
19. Ya amincewa hukumar ƴan yi wa ƙasa hidima (NYCS) ta shigar da ɗaliban buɗaɗɗiyar jami’a ta ƙasa (National Open University) cikin tsarin yi wa ƙasa hidima.
20. Ana sa ran zai ƙaddamar da mashinan iskar gas kashi na farko nan da ranar 29 ga watan Mayu, 2024.
21. Ya amince a aiwatar da tsarin kula da tallafi kan kiwon lafiya na ƙasa.
22. Ya amince da ayyukan inganta fannin ilimi.
23. Ya amince da manhajar bindiddigi ta ƴan ƙasa domin ba wa ƴan Najeriya damar taka rawa a harkokin siyasa.