Labarai

An Kama Wanda Ya K@she Alhaji Bello Bukar Adamu

Ke Duniya: An Kama Wanda Ya K@she Alhaji Bello Bukar Adamu

Matashin mai laifin Sadiq Zubairu, dan unguwar Hotoro Yandodo ne, mai shekara 35 a duniya, wanda ya hada baki tare da wasu mutane biyu, inda ya yaudari Abokinsa na kut Bello Bukar Adam mazaunin Zawachiki dan shekara 45 a duniya, zuwa gidansa.

Bayan yaje gidan nasa da motarsa kirar Toyota Corolla, sai kawai suka daure shi, sanann ya rinka dukansa da Muciya, ya rika kuma dora masa dutsen Guga akansa har sai da ya ce ga garinku nan.

Ganin haka tasa ya saka g@warsa cikin bayan motar Marigayin ya tafi can Titin bypass na Hotoro ya jefar da ita.

A sakamakon rahoton rashin ganin Marigayin da yayansa ya kai ofishin yansanda hakan tasa aka fara zurfafa bincike, kuma daga bisani aka samu labarin ganin gawar Marigayin ya she a gefen Titi, aka garzaya da ita Asibiti aka tabbatar da mutuwarsa.

Bayan kama Sadiq Zubairu ya tabbatar da aikata danyen aikin Kuma ya ce abunda ya sashi aikata wannan ta’asa shi ne, ganin ya yaudari Marigayin tare da karbar naira milyan 3 a hannun marigayin da sunan zai samo masa wani aiki, amma da ya fahimci ba zai iya mayar masa da kudin ba, kawai sai ya dauko wadannan mutane yan ina da kisa, suka yi ta’adin tare.

Yanzu haka yana komar rundunar yansandan Kano, kamar yadda kakakin su Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Jama’a Allah ka raba mu da mugun ji da mugun gani, Ka tsare mu da yin mu’ammala da bata gari.

 

Back to top button
error: Content is protected !!