Kannywood

Na Shafe Shekara Guda A KannyWood Amma Haryanzun Da Budurci Na

Na Shafe Sama Da Shekara Ɗaya Da Rabi A Kannywood Amma Har Yanzu Ina Tareda Budurcina Na, Céwar A’isha Shushu

Matashiyar Jaruma a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ai’sha Shushu ta bayyana cewa yau ta shafe sama da shekara ɗaya da rabi a Kannywood amma babu wanda ya taɓa riƙe ko da hannunta da zimmar wani abu. Kuma ko a yau ta samu mijin aure wanda shi ma bai taɓa sanin wata ƴa mace ba za ta aure shi.

Aisha Shushu

A’isha ta bayyana haka ne a ya yin wata tattaunawarta d Dokin Karfe TV inda ta nuna cewa ba duka aka taru aka zama ɗaya a masana’antar Kannywood ba.

Tunda farko A’isha ta fara ne da maida martani ga masu zargin ana lalata ƴan mata a Kannywood inda ta bayyana cewa:

“Waɗanda su ke faɗin cewa ƴan Kannywood na lalata tarbiyyar samari da ƴan mata ƙila kalar waɗannan su ka haɗu da su kenan, amma ni ka ga shekara ta ɗaya da rabi a Kannywood yanzu haka, na shigo da budurcina kuma har yanzu budurcina na nan, babu wanda ya taɓa riƙe ko da hannuna da zimmar wani abu”. A cewarta.

Daga nan A’isha ta ƙara da cewa: “Ko a yau na samu miji wanda shi ma haka ya ke, bai taɓa sanin wata ƴa mace a rayuwarsa ba, zan aure shi. Wanda bai taɓa aure ba, kuma bai taɓa sanin wata ƴa mace ba,”. Cewar A’isha Shushu.

Me zaku ce ?

Back to top button
error: Content is protected !!