Labarai

Kungiyar ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Dade Tanayi

Da Dumi – Dumi: Kungiyar malaman jami’a a Najeriya, ASUU ta sanar da jinkirta yajin aikin da mambobinta suka shafe wata takwas suna yi.

Dokta Chris Piwuna, mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU ya tabbatar wa BBC labarin, inda ya ce an janye yajin aikin ne da sanyin safiyar yau Juma’a, bayan da shugabannin kungiyar suka gana cikin dare a Abuja babban birnin kasar.

Kotun kolin Najeriya ta umarci kungiyar ta janye yajin aikin gabanin ta saurari daukaka karar da ta yi a gabanta. Tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar malaaman jami’o’in gwamnatin tarayyar Najeriya suka tsunduma cikin yajin aiki, suna neman gwamnatin ta biya musu wasu bukatu.

Back to top button
error: Content is protected !!