Yanda Kayan Masarufu Su Fara Sauka Daga Tsadar Da Suyi
Yanda Manyan Abubuwan Da Ake Amfani Da Su Duk Sun Fara SauKa!
A KULA!!!
Wannan farashin ba na shaci-fadi ba ne, Mai shakku na iya kiran kasuwa ya tabbatar!
Dalar da ta kai 1950 ta sauka zuwa 920
Dizil ya sauka daga 1600 zuwa 1200
Cement ya sauka daga 12500 zuwa 7000
TikitinJirgin sama daga Abuja zuwa Lagos ya sauka daga 195,000 zuwa 110,000
Indomi ta sauka daga 17000 zuwa 11000
Shinkafa Bigbull ta sauka daga 76000 zuwa 6800
Abubuwan da muke so a lura da su su ne:
Wannan rikitowar farashi na ababen da ake amfani da su a yau da kullun ba fa shi kenan ba, farawa suka yi kuma da su da ma wasun su za su ci gaba da sauka.
A karon farko an sami tsarin da ya karya al’adar nan ta cewa babu farashin abinda ke hawa ya sauka a Najeriya, kenan sai a mulkin Asiwaju.
Idan har wasu ‘yan kasuwa sun fara saukar da farashi wasu kuma sun ki, ya kamata mu yarda cewa lamarin yanzu yana hannun ‘yan kasuwa ne ba gwamnati ba.
Ya kamata mu san cewa wannan alhairi ne ya sami kasar mu Najeriya ba wai gwamnati zalla ba, Don haka me zai hana mu yada abin farinciki kamar yadda muka yada bakinciki a watan jiya da shekaran jiya?