Labarai

Daga Yanzu Ba Ni Da Wata Alaka Da Su Umar Bush,

Daga Yanzu Ba Ni Da Wata Alaka Da Su Umar Bush, Cewar Ibrahim

Ga abinda Ibrahim ya rubuta;

“Assalamu Alaikum

Dangane da batun alakar mu da Umar Bush da Sadiq ina mai sanarwa ‘yan uwa da abokan arziki cewa ni Ibrahim Abdullahi kamar yadda aka san muna yin bidiyo tare da Umar Bush da Sadiq a baya.

Daga yanzu ba ni da alaka da duk wasu bidiyoyi da ake yi wa Umar Bush ko nema masa lafiya, ko nema masa taimakon kudi, ko zuwa wani waje tare da shi.

Jama’a ku shaida a halin yanzu akwai wadanda suke yin aiki tare da su kuma tare da yardar iyayensu don haka ina yi musu fatan alkairi kuma zumuncina bai yanke da su ba, amma dai batun bidiyo na daina babu hannuna a ciki.

Nagode.

Back to top button
error: Content is protected !!