Jaruman KannyWood Mata Dasu Dade Gidan Mazajensu
Jaruman KannyWood Mata Da Ake Yaba Musu Saboda Dadewa Da Suyi A gidan Mazajensu. Ga Masu Cewa Matan KannyWood Basa Son Zaman Aure, Wadannan Jaruman Sun Tabbatarwa Da Duniya Cewa Wannan Maganar Da Akeyinta Ba GasKiya Bane.
Da Yawan Mutane Suna Dauka Cewa Dukanin Wata Jarumar Masana’antar KannyWood Idan Tayi Aure Bazata Iya Zaman Aure Ba, Inda Aka Maida Abun Kamar Cewa Ana Basu Wasu Watanni Kawai Sunayin Auren Zasu Fito.
A Haqiqanin GasKiya Wannan Tunanin Ba GasKiya Bane, Domin Kuwa Akwai Wasu Daga Cikin Shahararrun Jaruman KannyWood Mata, Wanda Tauraruwarsu Ta Haska Sosai Amma Kuma Har Yau Suna Dakin Mazajensu Na Aure Ba Tare Da Sun Fito Ba. Kamar Yadda Mutane Ke Yawan Tunani.
A Yanda Da Yawan Mutane Su Dauka Shine, Iya Jaruman KannyWood Mata Ne Kawai Basu Iya Zaman Aure, Ba Tare Da Sunyi Tunanin Cewa Ba Iya Su Kadai Bane Hakan Ke Faruwwa A Kansu. Akwai Da Yawa Daga Cikin Mata A Gari, Wanda Basu Iya Zaman Auren Kwata Kwata Amma Da Yake Su Ba.a Sansu Ba. Ba.a Magana Akansu.







