Labarai

Kadan Daga Ayyukan Shugaba Tinubu Cikin Shekara Daya

Kadan Daga Nasarorin Da Shugab Kasa Ahmad Bola TINUBU Ya Samar Cikin Kasa Da Shekara 1

DAGA Aliyu Samba

Wani arashi da muka samu a mulkin Shugaba Tinubu, a yanzu tsabar kuɗi na Naira ne kuɗin da ya fi kowanne kuɗi samun daraja (Performing Currency) a duniya kamar yadda Goldman Sachs Group suka bayyana.

A wannan lokacin na Mulkin Shugaba Tinubu ne aka samu nasarar kama yan ta’adda masu garkuwa da mutane da dama tare da yi musu shari’a a kotu da tabbatar da an musu hukuncin, saɓanin gwamnatin baya da bata taba ɗaure wani ɗan bindiga ba.

A wannan lokaci na mulkin Shugaba Tinubu, kullum ranar aiki ce yanzu a jihohin Kudu maso gabas. Zaman gida da yan ta’adda suka ƙaƙabawa al’ummar yankin ya zama tarihi.

A wannan lokaci na Mulkin Shugaba Tinubu, fargabar ta’addancin yan Boko Haram ta yi ƙaranci a Arewa maso gabas na ƙasar nan.

A wannan lokaci na Mulkin Shugaba Tinubu, shigo da tataccen mai zuwa kasar nan daga kasashen waje ya ragu da kimanin kaso 50 cikin 100.

A wannan lokaci na Mulkin Shugaba Tinubu, matatar mai ta Dangote da na Fatakwal zasu zaftare farashin Man Dizal nan da watan Mayu dake gabatowa, sannan kuma rage farashin man fetur zai biyo baya.

A wannan lokaci na Mulkin Shugaba Tinubu aka yi yarjejeniyar jigilar yan Najeriya kai tsaye daga nan har birnin Landan ta jirgi mallakin ɗan Najeriya (Air Peace).

A wannan lokaci na Mulkin Shugaba Tinubu, GDP din Najeriya ya ƙara hawa samun cigaba da kashi 3.4 cikin 100.

A wannan lokaci na Mulkin Shugaba Tinubu an kawo ƙarshen matsalar ƙarancin Fasfo, ana samun damar yin fasfo ga ƴan Najeriya cikin sauƙi kuma da wuri.

Duk da baza mu iya hana ƴan adawa faɗar abinda suke so ba na sukar gwamnatin Shugaba Tinubu ba, amma mun tabbatar da cewa yana kan cika mana burin mu na sabuwar Najeriya, kuma muna alfahari da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da ƙimar Najeriya a idon duniya. Shekara guda ta Tinubu ta kawo cigaban da shekaru 8 baya basu iya kawowa Najeriya ba.

Mun gode Baba Tinubu.

Back to top button
error: Content is protected !!