Daliban FUG Sun Tsira Bayan Yan Bindiga Sun Sake Su
Daliban FUG Sun Tsira Bayan Yan Bindiga Sun Sake Su.
Godiya ta tabbata ga Ubangijin da shi kadai ne mai ba da tsaro da aminci, wanda a karkashin mashi’ar sa da kudurar sa ragowar dalibban FUG su 22 ( Dalibbai 15, Ma’aikata 7) su ka samu ‘yanci daga azzaluman da su ka yi garkuwa da su tun a cikin watan September na shekarar da ta gabata ta 2023.
Godiya da jinjina ga hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya da su ka yi ruwa da tsaki ganin wadan nan yara sun koma hannun iyayen su lami lafiya.
ABUN LURA.
Da wahala ace ta hanyar amfani da karfin bindiga aka kubutar da wadan nan dalibbai face ta hanyoyin lalama da tatattaunawa, don haka mu ke fadar cewa ba kowane lokaci kuma a kowane irin yanayi amfani da karfin bindiga ke samar da kyakkyawan sakamako ba.
Ya ishe mu misali da haramtacciyar kasar Isra’ila akan yakin zalunci da ta ke yi da fararen hulla na kasar Palestine. Duk da karfin sojan Isra’ila da yawan makaman su amma sun yarda da sasanci irin na tsagaita bude wuta na wucin gadi domin a saki mutanen su da HAMAS ke rike (garkuwa) da su inyasso daga bisani sai a koma fagen fama.
A karkashin irin wannan yanayin ne gwamnatin HE Matawalle da ta gabata ta bullo da tsarin “Carrot and Stick Approach” da kuma “Kinetic and Non Kinetic Approach”, wato inda ya kamata a yi amfani da sulhu/sasanci/lalama/tattaunawa sai ayi, inda kuma ke bukatar fito-na-fito sai ayi.
A irin wannan yanayi da aka yi garkuwa da dalibban FUG, abu ne mai wahala a kubutar da su duka ba tare da “Collateral Damage” ba, don haka a irin wannan yanayin ba laifi ba ne don anbi hanyoyin lalama inyasso bayan kubutar da su sai a koma fagen yaki tsakanin gwamnati/jami’an tsaro da ‘yan ta’adda.
Allah Ta’ala ya kare sake afkuwar wannan lamari.
Allah dawo mu na da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
IBG
16/04/2024