Labarai

Ministan Noma Ya Halarci Taro Kan Harkokin Noma

Ministan Noma Ya Halarci Taro Kan Harkokin Noma A Ƙasar Maroko.

Noma

Ministan noman Najeriya, Sen. Abubakar Kyari, CON, yana halartar taron ƙungiyar noma na majalissar ɗinkin Duniya na yankin Afrika a birnin Rabat na ƙasar Maroko wanda aka fara a yau 18 zuwa 20 ga watan Afrelu, 2024.

Taken taron na bana shi ne “rungumar noma da zamanantar da cigaban yankunan karkara” wanda ya ƙunshi taɓo ƙalubalen da noma ke fuskanta a Najeriya a fannin samar da wadataccen abinci.

Taron ya ba da damar samar da wani zaure na haɗin gwiwa da ƙulla alaƙa a matakin ƙasa da Larduna domin daƙile wannan ƙalubale. Najeriya za ta amfana da alaƙa da ƙwararru, kayan aikin noma na zamani da kuma tallafi ga manoma.

A cewar minista Kyari, Najeriya ta himmatu wajen aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ƙungiyar domin ribatar ƙirƙire-ƙirƙire da fasahohin zamani domin wadata ƙasa da abinci zuwa gaba. Rungumar tsare-tsaren dama ce ta haifar da wani juyin-juya-hali a fannin noman abinci tare da tabbatar da samuwar amfani mai kyau da gina jiki gami da kula da muhalli da kyautata rayuwar al’umma gabaɗaya.

“Haɗin-gwiwarmu da FAO, musamman kan tsarin shirin haɗa hannu tare a Jihohi irin su: Katsina, Borno, Niger, Cross River, Ebonyi, da Jihar Oyo, zai haifar da kykkyawan sakamako”. Cewar minista Kyari.

Ministan ya kuma yi nuni da muhimmancin da ke tattare da yin musayar ƙwarewa da ilimummukan da aka koya musamman ƙarƙashin shirin haɗa hannu tare ta hanyar musayar tattaunawa da kayayyakin kasuwanci, tare da tabbatar da cewa za su ƙara ƙaimi domin tabbatar da cewa abinci ya wadata a ƙasa gami da ɗaga cigaban yankunan karkara a Najeriya da yankunan Afrika gabaɗaya.

Back to top button
error: Content is protected !!