Labarai

Abin Da Yasa Kotu Ta Tsare Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi A Kurkuku

Dalilan Da Yasa Kotu Ta Tsare Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi A Kurkuku!

Wata kotun Majistare a Bauchi ta ba da umarnin tsare wani fitaccen malamin addinin Muslunci a jihar, Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi a gidan yari.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ce ta gurfanar da malamin mai janyo taƙaddama a gaban kotu ranar Litinin, bayan ta gayyace shi game da wani ƙorafi a kan malamin.

Matakin na zuwa ne sama da wata ɗaya bayan

A ranar 8 ga watan Afrilu ne, Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi ta yi ƙarin haske a kan matakinta na ɗage wani zaman tattaunawa da ta shirya da Sheikh Idris Abdul’aziz, wanda aka yi zargin ya furta wasu miyagun kalamai a kan Annabi Muhammadu.

Ana zargin fitaccen malamin ne da furta kalamin cewa ‘ba ya buƙatar taimakon Annabi’, abin da mafi yawan mutane ke ganin, munana lafazi ne kuma bai nuna biyayya ga Fiyayyen Halitta ba.

Lamarin ya janyo muhawara mai zafi da ka-ce-na-ce har a tsakanin malaman addinin Musulunci da ke arewacin Najeriya, inda wasu suka fara kiraye-kirayen lallai hukumomi su ɗauki mataki.

Lauyan malamin Bar, Umar Hassan ya tabbatar da cewa an tsare malamin, bayan sun nemi a bayar da belin sa, inda kotu ta sanya Talata a matsayin ranar da za ta ba da hukunci a kan wannan buƙata.

Daga Shafin BBCHausa

Back to top button
error: Content is protected !!