Kannywood

Dalilin Da Yasa Na Fito Na Bayyanawa Duniya Halin Da KannyWood Ke Ciki

Jarumi Abdullahi Amdaz Na Fuskantar Kalubale Daga Abokan Sana’arsa Na (KannyWood) Tun Bayan Tonawa Harkar Sana’arsa Nasu Asiri Da Yayi.

Abdullahi Amdaz Adam A Zango On Set

Jarumi Kuma Mawaƙi A Masana’antar KannyWood, Abdallah Amdaz, Ya Fara Fuskantar Ƙalubalantar Da Tsana Daga Abokan Sana’arsa Nashi, Inda Wasu Ke Ikirarin Cewa Ya Bata Musu Suna, Don Haka Zasu Daina Saka Shi A Cikin Fina Finai, Harma Wasu Daga Cikinsu Na Barazanar Gurfanar Dashi A Gaban Shari’a.

A Ranar Litinin Data Gabata Ne Abdallah Amdaz Ya Bayyana Wasu Dabi’u Marasa Kyau Da Wasu Yan Masana’antar KannyWood Din Ke Aikatawa, A Wajen Taron Da Hukumar Hisbah Na Jihar Kano Karkashin Jagorancin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Ta Shirya Da Yan Masana’antar KannyWood.

Sai Dai Jarumin Yace Ya Bayyana Abubuwan Da Ya Fada Bawai Don Cin Mutunci Ko Cin Fuska Ba. Shi Ya Bayyana Ne Saboda Yadda Shugaban Hukumar Hisbah Daurawa Yace Su Fadi Tsakaninsu Da Allah Kan Duk Wasu Matsalolin Da Suke So A Gyara, Wanda Yace Shi Kuma Yana Ganin Yan Fim Yan Uwansa Ne, Bai Kamata Su Je Lahira Su Na La’antar Junansu Ba, Gwanda Tun A Duniya Ya Bayyana Gaskiya, Tunda Dai Abincinsa Da Ɗaukakar Sa Na Hannun Allah.

Kalli Cikakken Bidiyon Hirar Da Abdullahi Amdaz Din Kan Dalilin Da Yasa Ya Fadi GasKiya A Gaban Shugaban Hisbah Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa.

Back to top button
error: Content is protected !!