Kannywood

Zan Rataye Kaina Idan Banyi Ido Biyu Da Momme Gombe Ba

Momee Gombe

Wannan Matashin Ya Sha Alwashin Rataye Kansa Idan Har Bai Yi Ido Biyu Da Jarumar Fim Din Hausa, Momme Gombe Ba

Nura Habibu wani matashi dan jihar Kano ya yi rantsuwa cewa indai wannan rana 20/8/2020 ta wuce bai yi ido biyu da jarumar finafinan Hausa Momme Gombe ba, to babu shakka sai ya kashe kanshi ta hanyar rataya.

Saidai ita Momme Gombe ta yi rubutu a shafinta na Facebook tana cewa ka sani cewa kai musulmi ne idan ka aikata haka ba ni da aljannar da zan saka ka. Sannan ta kara da cewa idan kana son gani na ba sai ka biyo ta wannan hanyar ba.

Back to top button
error: Content is protected !!