Labarai

Shugaba Tinubu Zai Saka AC A Masallacin Abuja

Shugaban ƙasa Tinubu ya ɗauki nauyin saka AC a babban masallacin Juma’a na ƙasa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki nauyin sanya na’urorin sanyaya wuri (air conditioners) a babban masallacin ƙasa da ke Abuja (National Mosque) daga aljihunsa.

Da yake jawabin godiya ga malamai da al’ummar da suka halarci taron addu’a da aka gabatar a masallacin domin yiwa Shugaban ƙasa da Najeriya addu’a a ranar da Shugaba Tinubu ke cika shekaru 72, mataimakin shugaban ƙasa ya ce Tinubu mutum ne mai kyauta da karamci.

“Shugaban ƙasa mutum ne mai kyauta irin wadda addini ya koyar, wato ya bayar da hannun dama ba tare da hagu ta sani ba. Kamar yadda wasu a nan suka sani, ya bayar da gudunmawar ƙashin kansa ta Naira miliyan 250 domin sake gina babban masallacin Zaria.

“A yanzu kuma, duk da ya ce kar na faɗa a fili, ina farin cikin sanar da ku cewa shugaban ƙasa ya ce zai ɗauki nauyin sanya AC a wannan masallacin saboda ganin halin da masallata ke shiga saboda zafi,” in ji Sanata Shettima.

Malaman ɓangarorin addinin musulunci daban-daban ne suka jagoranci zaman addu’o’in inda aka roƙa ƙasa zaman lafiya da cigaba tare da yiwa shugaban ƙasa fatan samun ƙoshin lafiya da sa Najeriya bisa doron cigaba.

Back to top button
error: Content is protected !!