E News

Ministan Noma Na Najeriya Ya Halarci Taro Da Gwamnan Filato

Ministan Noma Na Najeriya Ya Halarci Taro Da Gwamnan JIHAR Filato

A yayin taron, mai girma ministan noma na Najeriya, Sen. Abubakar Kyari CON, ya yi wa gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ta’aziyyar mutanen da suka rasa rayukansu a rikici na baya-bayannan da ya faru a Jihar tare da yaba masa bisa gagarumar gudunmawarsa.

A cewar minista Kyari, gwamna Mutfwang shi ne gwamna ɗaya tilo da ya kasance a wajen gasar ba da lambobin yabo kan abinci ta Duniya wanda aka gudanar a Lowa, a watan Oktoban 2023. Ya kuma nuna buƙatar da ake da ita ta samar da haɗin gwiwa da gwamnonin Jihohi domin tunkarar matsalar canjin yanayi da matsalar tsaro dake shafar fannin noma. Ya kuma nuna shirin samar da tsarin ƙara wa dabobi daraja a Jihar Filato.

Shi ma a nasa tsokacin, gwamna Mutfwang ya yabawa minista Kyari game da ƙoƙarinsu na magance matsalar ƙarancin abinci a ƙasa tare da bayyana ƙwarin gwiwarsa kan ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin cigaban fannin noma. Ya kuma bayyana matsayin da Jihar Filato take da shi a fannin noma wanda kuma take taka gagarumar rawa wajen samar da dankalin turawa.

Sannan kuma gwamnan ya ƙara na’am da batun tabbatar da haɗin gwiwar aiki tare da ma’aikatar noma ta ƙasa domin cigaba da zamanantar da fannin noman Najeriya yayi gogayya da na ƙasashen da suka cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!