Kannywood

Shigar Shirin MATI A ZAZZAU Netflix Babban Nasara Ce

Shigar Shirin MATI A ZAZZAU Manhajar Netflix Babbar Nasara Ne Ga Masana’antar Shirya Fina Finai Na Hausa. Ba Iya Rahama Sadau Ba.

Ana ci gaba da jinjina da kwarzanta ƙoƙarin masu shirya fim ɗin ‘Mati A Zazzau’ wanda ya buɗe ƙofa ga Kannywood, bayan ya zama fim ɗin masana’antar na farko da ya shiga manhajar Netflix.

A ranar 31 ga Disamban 2023 ne, manhajar nuna fina-finan kai tsaye ta intanet a duniya, ya ƙaddamar da fim ɗin na farko daga Kannywood, inda masu sha’awar kallo daga ko’ina a duniya za su iya samu cikin sauƙi su kalla.

Wata majiya daga Kannywood ta shaida wa BBC, an shafe tsawon lokaci, ana yunƙurin ganin katafaren kamfanin nuna fina-finan kai tsaye ta intanet a duniya ya karɓi, shirye-shiryen Kannywood, ba tare da an yi nasara ba, sai a yanzu.

Mati a Zazzau, wanda ci gaba ne na fim ɗin Mati da Lado ne, ya fara fitowa ne tun ranar 7 ga watan Fabrairun 2020.

Shigar Mati a Zazzau manhajar Netflix, wata gagarumar nasara ce ga Kannywood, kuma hakan zai sanya fina-finan Hausa su yi gogayya da takwarorinsu na duniya musamman masana’antar kudancin Najeriya wato Nollywood.

Jaruma Rahma Sadau da jarumi Sadiq Sani Sadiq ne suka shirya shi, yayin da Yasseen Auwal ya ba da umarni.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwar fina-finai ta koma manhajojin intanet, inda masu shirya fim suka raja’a a kan dandalin Youtube wajen nuna shirye-shiryensu.

‘Nasara ce ga Kannywood’

A cewar marubuci kuma mai sharhin fina-finan Kannywood, Mallam Ibrahim Sheme, matakin da Mati a Zazzau ya taka, babu wani fim ɗin Hausa da ya taɓa kai wa.

Kasancewar Netflix ne dandalin kallon fim mafi girma, ba kamar a baya ba, lokacin da sai dai a je silimar unguwa, ko kuma mutum ya sayi fim kaset ko faifan sidi domin kallo, yanzu a duk inda mutum yake a kusurwar duniya, zai iya gani, in ji Sheme.

”Wannan mataki da fim ɗin ya kai wanda shi ne na farko daga Kannywood, ba ƙaramar nasara ba ce ga masana’antar. ”

Ya ce Rahama Sadau kuma ta karya wani ƙwari, kasancewar akwai furodusoshi da daraktoci masu yawa da suka yi ta buri da fafutukar yin fim ɗin da zai kai wannan matakin, amma hakan ba ta samu ba.

A cewarsa: “ƴan’uwanmu na kudancin Najeriya sun jima da kai wa wannan mataki, amma mu sai a watan Disambar bara, Rahama ta samu damar shigar da fim ɗinta, don haka nasarar ba ta Rahama kaɗai ba ce, ta kowa da kowa ce da ke wannan masana’anta”.

Rashin sanin inda za a hau a sauko, na daga cikin dalilin da ya sa aka ɗauki lokaci kafin hakan ta tabbata.

Ina alfahari da zama daraktan Mati a Zazzau’

Daraktan da ya ba da umarni a fim ɗin Mati a Zazzau shi ne Yasseen Awwal, ya shaida wa BBC cewa farin cikinsa ba zai taɓa misaltuwa ba, ganin wannan ne karon farko da Kannywood ta taka matsayi irin hakan.

“Idan akai la’akari da matsayin da muke yin fina-finan Kannywood, kowa na da burin ya kai wannan mataki, hakan ya nuna fim ɗinmu ya kai mizanin duniya baki ɗaya, saboda haka farin cikina ba zai misaltu ba.”

Ya kuma ce matuƙar mutum na iya shiga ya fita a inda ya dace, to ba shakka zai iya kai wa ga nasara, Rahma Sadau ta bada gudummawa sosai domin ganin wannan fim ya kai matakin shiga Netflix,’’ in ji Yassen.

A karshe ya ce fatansa ga Kannywood shi ne su ci gaba da jajircewa wajen samar da labarai, da kayan aiki da ɗaukar ƙayatattun shirye-shirye da fina-finai masu inganci, ta yadda za a riƙa samun fina-finan Hausa da za su kai matakin kallo a manhajar duniya ta Netflix.

‘Rahama ta buɗe wa Kannywood hanya’

Rahama Sadau dai, fitacciyar jaruma ce kuma ta yi ƙaurin suna a Kannywood kan janyo ka-ce-na-ce, kama daga waƙar da suka yi da mawaƙi Classic da ta janyo dakatar da ita a masana’antar.

Da korafin da ake yi kan irin salon sanya tufafinta a wasu lokuta.

Malam Ibrahim Sheme ya ce ba ya tababa a kan Rahama Sadau za ta ci gaba da bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen bunƙasa Kannywood da kawo ci gaba a masana’antar.

”Wani abu da nake son a fahimta a nan shi ne, Netflix suna sayen fim ne daga hannun mai shi, kuma ƙaramin farashin da suke saya yana kamawa daga dala 10,000 zuwa 20,000 akwai wanda zai iya kai wa dala 100,000.”

Ya ce ya yi imani duk abin da Rahama Sadau ta samu, za ta sake zubawa ne a Kannywood, domin sake shirya wani fim ɗin da za ta yi ƙoƙarin ganin ta kai shi wannan ƙololuwar ɗaukaka, in ji Sheme.

Me Netflix ya ce?

Tun a ranar Lahadi 31 ga watan Disamban 2023, kamfanin Netflix ya wallafa samfoti ko ɗanɗano jiran rabo na fim ɗin Mati a Zazzau a shafukansa na sada zumunta, inda yake sanar da masu kallo cewa ya ɗora musu fim na Hausa.

Yana cewa: “Ko Mati zai gano dukiyar mahaifinsa da ke ɓoye? Mati a Zazzau yanzu ana iya kallonsa kai tsaye”.

Daga Shafin BBCHausa

Back to top button
error: Content is protected !!