E News

Martanin Aisha Humaira Kan Kidaya Challenge

Masu Sukar Gasar Waƙar Ƙidaya Ta Rarara, Kwakwalwar Dusa Ce A Kan Su – Cewar Ta Hannun Damar Dauda Rarara Kahutu Wato Aisha Humaira

Aisha Humaira Rarara Kidaya Challenge

Jarumar Masana’antar Shirya Fina-finan Hausa Na Kannywood, Kuma Abokiyar Aikin Mawaƙin Siyasa Dauda Kahutu Rarara, Wato Aisha Humaira, Tayi Kaca-Kaca Da Wasu Jaruman TikTok Da Kuke Sukar Gasar Waƙar Ƙidaya Da Rarara Ya Rera,

Inda Tace Akwai Wadanda Dusa Ce Ko Katako Ne A Kan Su, Akwai Kuma Wadanda Za’a Iya Yiwa Uzuri Domin Basu Fahimci Abinda Ake Nufi Da Ƙidaya Ba.

Aisha Humaira Wacce Ta Bayyana Haka Cikin Wani Faifen Bidiyo A Manhajar Tiktok Din, Inda Tace Dama Halayyar ‘Yan Arewa Ne, Su Soki Duk Wani Abu Mai Kyau Da Ɗan Uwansu Ya Fito Dashi.

Tunda Farko Dai Wasu Ma’abotan Na Shafukan Sada Zumunta Ne Su Soki Batun Na Gasar Waƙar Ƙidaya Ta Rarara, Bisa Hujjar Cewa Bai Yi Waƙar Janyo Hankalin Mahukunta Akan Sha’anin Tsaro A Yankunan Da Ake Fama Da Matsalar Tsaro Musanman Ma Arewacin Nigeria, Kuma Bai Shiga Cikin Kiraye-kirayen Da Ayi Kan Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro Musamman A Arewacin Najeriya.

 

 

Back to top button
error: Content is protected !!