E News
An Kwato Naira Biliyan 30 Tare Da Asusu 50 Na Banki Daga Wajen Better Edu
An Kwato Naira Biliyan 30 Tare Da Asusu 50 Na Banki Daga Wajen Better Edu – EFCC
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta kwato Naira biliyan 30 a kan zargin karkatar da kudaden da ake zargin ministar jin kai, Betta Edu da aka dakatar.
Har ila yau, an bayyana cewa a halin yanzu ana binciken asusun ajiyar banki 50.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai suna, “EFCC Alert.”
Sanarwar ta yi cikakken bayani kan wasu manyan tsare-tsare da gurfanar da su gaban kuliya da kuma kwato kudaden da hukumar ta yi a cikin watan jiya.
Takardar da Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa N30bn da aka kwato yanzu haka suna cikin asusun gwamnatin tarayya.