E News

Hukuncin Shekara Daya A Gidan Yari, Ko Tarar 500K

Hukuncin tsokanar marasa lafiyar kwakwalwa ya kai shekara ɗaya a gidan yari ko tarar N500,000. Jama’a mu kiyaye.

Inji Shahararren Lauyan Nan Na Jihar Kano. Wato Abba Hikima. Inda Ya Rubuta A Shafinsa Kamar Haka.

Babu ranar da mutane baza suyi tagging ɗina akan abunda ake yiwa wannan bawan Allahn ba. Yau wani likita ya biyo ni har inbox ya ɓuƙaci a ƙara jan hankalin masu tsokanarsa saboda lafiyarsa.

Kwanakin baya nayi magana akan sa inda na roki masu tsokanarsa su daina duba da cewa akwai rashin lafiya a tare da shi, kuma ashariyar da ake sawa yana yi domin saka wasu nishaɗi ba abun so bane, amma sai masu amfana da rashin lafiyarsa suka sa shi yayi min video yana cewa “shi video yanzu ma aka fara yi masa”. Saboda na lura daga shi har masu tsokanar tasa suna amfana da rashin lafiyarsa.

To har yanzu dai ina kara kira a gare mu baki ɗaya. Na tabbataba idan ɗan’uwanmu ne baza muso abunda ke faruwa ba.

Idan zamu taimake shi saboda Allah muyi. Amma wannan abun bai dace ba. Amma lallai in ba’a daina ba zamu dau matakin da ya dace.

Back to top button
error: Content is protected !!