Kannywood

Zargin Madigo: Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta zagba mata mari

A cikin ‘yan kwanakin nan ne aka rika yada wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ke nuna yadda jaruman Kannywood Hadiza Gabon ta rika shararawa jaruma Amina Amal mari tare da tsangwaman ta a daki tana mata tambaya a kan wani tes da ta aika mata.

A cikin bidiyon, an rika jin muryar da akayi ikirarin na Gabon tana cewa a bari ta yiwa Amal dukan tsiya saboda wai tayi mata sharri yayin da ita kuma Amal tayi zugum zaune a kan gado tana sauroron Gabon tana ba ta hakuri.
Amal din ta rika fada wa Gabon cewa ta yafe mata domin kuskure ne inda hasali ma ta ce ita ba ta san lokacin da ta aika wannan sakon ba a yayin da ta ke tilasta mata ta karanta sakon.
Wani da ke tare da Gabon a wurin ya yi kokarin hana ta cigaba da dukan Amal amma hakan ya ci tura inda daga bisani shine ya karanta sakon.
“Salam, Yar uwa ta, don Allah idan ba kya komai anjima ina son ganin ki, ma’assalam.” kamar wani aka karanto sakon.
Al’umma sun rika bayyana mabanbanta ra’ayoyinsu a kan lamarin inda wasu suka ce abinda Gabon ta aikata zalunci ne da fin karfi wasu kuma suka rika yi mata uzuri da cewa bacin rai ne ya janyo haka kuma hakan zai iya faruwa da ko wanne dan adam.
Hakan ya sa suka bukaci al’umma su dena ruruta wutan gaba tsakanin jaruman kuma abinda ya fi dacewa shine ayi kokarin sulhu tsakanin su.
An dade dai ana zargin wasu ‘yan Kannywood da madigo a tsakaninsu inda a shekarun baya wasu jarumai kamar Adam Zango da Mustapha Naburaska suka fito fili suka soki abin inda suka ce ba su cikin masu aikata wannan lamarin.
Ga bidiyon nan a kasa:
It looks like this video of Amina Amal has also gone viral. Gabon was asking her why she’s accused her in that Instagram post. We have to cropped the ending saboda bai kamata ba abunda aka ce. pic.twitter.com/rR6Gkwo5Mn

Back to top button
error: Content is protected !!