Zargin Da Ake Yi Min Na Almundahanar Naira Miliyan 585
Zargin Da Ake Yi Min Na Almundahanar Naira Miliyan 585 Yunƙurin Ruguza Ƙoƙarina Ne, Cewar Betta Edu
Betta Edu, ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, ta ce zargin wawurar Naira miliyan 585 da ake yi mata, wani yunƙuri ne da wasu mutane ke yi na kawo cikas ga ƙoƙarin da ma’aikatar ke yi na yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma ɗaukaka mabuƙata.
Betta Edu ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Asabar.
Ministan ta fuskanci suka sosai a ranar Juma’a bayan wata takarda ta bayyana inda ta umurci Akanta Janar na Tarayya Oluwatoyin Madein da ya tura Naira miliyan 585 zuwa wani asusu mai zaman kansa mallakin wata Oniyelu Bridget.
Ma’aikatar ta ce Oniyelu Bridget tana aiki a matsayin Akanta na Ayyuka, Tallafawa ga ƙungiyoyi masu rauni.
Sai dai da take tsokaci kan batun, Edu ta ce zargin cin hanci da rashawar ba shi da tushe balle makama.