Kannywood
Zan Zo Mu Daidaita, Ayi Dakan Daka Shikar Daka – Adam A Zango Da Hadiza Gabon
Tauraton fina-finan Hausa,Adam A. Zango ya bayyana muradinsa ga abokiyar aikinshi, Hadiza Gabon.
Adamu ya bayyana hakabe ta hanyar comment da ya yiwa Hadizar karkashin wani hoto data saka a shafinta na Instagram inda ya bayyana cewa:
Zango mu daidaita Dije….kinga shikenan dakan daka shikar daka tankaden bakin gado.
Hadizar dai martanin dariya kawai ta mayarwa da Zango.
A baya dai Rahotanni sun nuna cewa Adam A Zango yayi soyayya da jarumai mata irin su Nafisa Abdullahi da Fati Washa da kuma na kwanannan daya bayyana watau Asiya Ahmad da akewa Lakabi da Asiya Me kyau.