E News
Zan Kawo Ƙarshen Matsalar Hauhawar Farashi Nan Ba Da Jimawa Ba A Faɗin Najeriya
Zan Kawo Ƙarshen Matsalar Hauhawar Farashi Nan Ba Da Jimawa Ba A Faɗin Najeriya, Cewar Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa gwamnatinsa za ta shawo kan matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki da ƙasar ke fama da shi, ciki har da sauko da hauhawar farashin kayayyaki.
Ya ce duk da cewa shi ba na daban bane, amma kada ‘yan Najeriya su damu saboda yana da zimmar kawo ƙarshen hauhawar farashi.
Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi bakuncin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a wajen buɗe-baki a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba, inda ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru don sauko da farashin kayayyaki.