Zainab Indomie Ta Bayyana Irin Kalar Mijin Da Take So. Ya Aureta
Jaruma Zainab Indomie Ta Bayyana Irin Kalar Mijin Da Takeso Ya Aureta, Bayan Tasha Qalubalen Rayuwa.
Jarumar Dai Tayi Zamani Mai Tsayi A Masana’antar KannyWood, Inda Taja Ragama Na Lokaci Mai Tsayi A Masana’antar Kafin Ta Fara Fuskantar Qalubale Na Rayuwa.
A Wasu Shekaru Dasu Shude Ana Ganin Kamar Babu Wani Lokaci Ma Da Zaizo Ya Wuce Da Tauraruwar Jarumar Zai Dusashe, Sai Dai Lokaci Daya Kuma Jarumar Ta Sami Jarabawar Rayuwa Inda Komai Yazo Ya Tsaya Mata.
Domin A Shekaru Kadan Dasu Wuce An Nemi Jarumar Kwata Kwata An Rasa Ta, A Lokacin Ne A Dunga Yada Labarai Kala Kala Dangane Da Jarumar Inda Wasu Ke Cewa Zainab Indomie Aure Tayi, Wasu Kuma Ke Cewa Tayi Hatsarin Mota Har An Yanke Mata Kafa, Yayin Da Wasu Ke Yada Labarin Cewa Jarumar Ma Mutuw@ Ma Tayi Gaba Daya.
Sai Dai Bayan Yada Ire Iren Wadannan Labarun Ne Sai Jarumar Ta Fara Fitowa Duniya Ta Fara Ganinta, Inda A Yan Wasu Shekaru Aga Jarumar Ta Fara Fitowa A Wasu Fina Finai Duk Da Cewa Tauraruwar Jarumar Sun Dusashe.
Yanzun Haka Akwai Wasu Fina Finai Da Ake Shiryawa Da Jarumar Na Shoffin Ubannin Gidanta Wato Ali Nuhu Da Adam A Zango. Fina Finan Inda Sun Hada Da Asin Da Asin. Da Kuma Alaqa.
Jarumar Ta Bayyana Kalar Mijin Da Take Fatan Ya Aureta Domin Su Karasa Rayuwarsu A Tare, Ta Bayyana Hakan Ne A Hirar Da Akayi Da Ita Na Hadiza Gabon Talk Show.
Ga Bidiyon Bayanin Jarumar Inda Ta Bayyana Da Bakinta.