Kannywood

Za Mu Yaƙi Arewa24 Kan ɓarnar Da Ake Cikin ‘Kwana Casa’in’ – Afakallah

HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bayyana cewa ko da wasa ba za ta yarda tashar Arewa24 ta ci gaba da nuna shirin diramar nan na ‘Kwana Casa’in’ ba domin ya na ɗauke da abin da ta kira baɗala.
Haka kuma ta ce matsayin ta a kan lamarin ya yi daidai da dokar da ta kafa ta.


Shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), shi ne ya bayyana haka a hirar da ya yi da mujallar Fim ɗazu.
Ya ce zai maka Arewa24 a kotu idan har tashar ta bijire wa umarnin sa.
A jiya ne Afakallah ya umarci tashar talbijin ɗin da ta ɗage nuna wasannin ta biyu mafi farin jini ga ‘yan kallo, wato ‘Kwana Casa’in’ da ‘Gidan Badamasi’, domin ba a ba hukumar sa ta tace su ba kafin a watsa su a duniya.


A hirar sa da mujallar Fim a yau, Afakallah ya bayyana cewa idan har Arewa24 ba su bi umarnin ba, to hukumar za ta mata su a kotu.
Ya ce: “Lallai abin da mu ka yi ya na bisa doka, domin a yadda ake nuna shirin ya saɓa wa ƙa’idojin mu na addini da al’adun ƙasar Hausa.


“Don haka dole ne mu sauke nauyin da ya ke kan mu na kiyaye dokoki da ƙa’idoji, don bai kamata mu bar wannan ɓarnar ta cigaba ba.
“Wannan ya sa mu ka ba su lokaci da su dakatar da shirin tare da cire waɗannan wuraren masu nuna baɗala.”


Da wakilin mu ya tambaye shi idan hukumar tasa ta na da iko a kan gidan talbijin ɗin da ba a Kano shirye-shiryen sa su ka tsaya ba, sai ya ce, “To idan ma ba iya Kano ya tsaya ba, a ina ofishin su ya ke? Ta ina su ke yaɗa ayyukan nasu?
“Tun da a Kano su ke yi, ya zama dole su bi dokokin Kano, idan kuma ba haka ba sai mu je kotu, idan mun je sai a tantance.

“Mu dai a matsayin mu na waɗanda nauyin jama’a ya ke kan mu, mun fita haƙƙi, don haka ba za mu bari ana yaɗa ɓarna ba sai inda ƙarfin mu ya ƙare.
“Kuma jama’a shaida ne daga lokacin da aka fara nuna cigaban shirin, ka ji yadda ake ƙorafi saboda irin rungumar mata da ake yi.


“To idan mu ka bari, nan gaba ma za a nuno wajen da ake saduwa. Don haka ne mu ka ce a tsayar da shirin domin a cire abubuwan da ba su dace ba.”
Tun daga jiya dai matakin hukumar ya haifar da muhawara a cikin jama’a, musamman a soshiyal midiya, inda wasu ke suka wasu kuma na yabo.


Akwai masu cewa hukumar ta shiga hurumin da ba nata ba, yayin da wasu ke ganin abin da ta yi ya dace.


Masu sukar tashar sun yi nuni da wani waje a cikin ‘Kwana Casa’in’ da aka nuna a ranar Lahadi da ta gabata inda ‘yan daba su ka kamo hannayen wata yarinya su ka kawo ta gaban ogan su da ke tsaye a waje.
Wurin ne Afakallah ya ce maza sun rungumi mace.


A tsarin finafinan Hausa, ba a bari jikin mace ya shafi na mace ko ta halin ƙaƙa.
Tun jiya mujallar Fim ta ke ƙoƙarin jin ta bakin ɓangarorin biyu.


Wakilin mu ya ji wasu daga cikin ma’aikatan Arewa24, musamman ɓangaren masu rubuta labaran dirama, su na cewa za a ci gaba da nuna shirye-shiryen kamar yadda aka saba ba tare da an kai wa hukumar ta duba ba.


Wani daga cikin su wanda ya ce a sakaya sunan sa domin bai da ikon yin magana da yawun gidan talbijin ɗin ya ce Arewa24 ta yi rajista ne da hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta ƙasa (National Broadcasting Commission, NBC), don haka wata hukumar gwamnatin Kano ko ta wata jiha ba ta da ikon dakatar da wani shiri nata.

Back to top button
error: Content is protected !!