Za Ka Iya Auren Budurwar Da Wani Ya San Ta ‘Ya Mace?
Wata kotu a Bangladesh ta soke tambayar mace “ko ta san da namiji kafin aure?” a kan takardar rajistar aure.
Kungiyoyin kare hakkin mata da suka dade suna fafutukar a cire wannan tambaya- wanda a ganinsu cin mutunci ne- sun yi maraba da hukuncin kotun.
A wani bangaren kuma, kotun ta ce dole angwayen su bayyana idan suna da aure ko a’a.
Dokokin aure a Bangladesh, kasar da mafi yawan mutanenta musulmi ne, sun sha suka daga kungiyoyin kare hakkin mata a matsayin masu nuna bambanci.
Ana yi wa yara mata da yawa a kasar auren dole tun suna kanana.
Me kotun ta ce?
Kotun ta ce dole ne a cire kalmar “kumari” a harshen Bengali a kan takardun rajistar aure.
Ana amfani da kalmar ne wajen bayyana macen da bata taba aure ba, haka kuma kalmar na nufin “wanda bai taba yin jima’i ba”.
Lauyoyin kungiyoyin da suka shigar da karar a shekarar 2014 sun yi nasara wajen kafa hujjar cewa takardun na nuna cin mutunci sannan suna keta haddin mata.
Ranar Lahadi, kotun ta ce a yanzu dole ne a yi amfani da kalmar “obibahita” a harshen Bengali, wanda ke nufin “macen da ba ta da aure”, a maimakon kalmar “kumari”.
A wani hukuncin na daban, kotun ta bukaci angwayen su bayyana idan ba su taba aure ba, ko kuma sun rabu ne da matansu ko kuma matarsu ta rasu.
Ana sa ran sauye-sauyen za su fara aiki nan da ‘yan watanni lokacin, da za a wallafa cikakken hukuncin kotun a hukumance.
Me mutane ke cewa?
“Wannan wani babban mataki ne,” in ji Aynun Nahar Siddiqua, daya daga cikin lauyoyin da suka shigar da karar.
Ta ce tana fatan hukuncin zai taimaka wajen inganta hakkokin mata a Bangladesh.
A yanzu haka, wani mai rubuta takardar shaidar aure ya ce shi da abokan aikinsa na jiran hukumomi su sanar da su sauye-sauyen a hukumance.
“Na daura aure da dama a Dhaka kuma an sha tambayata dalilin da ya sa ba a yi wa maza irin wadannan tambayoyin. A kodayaushe ina gaya masu cewa abin ba a hannuna yake ba,” Mohammad Ali Akbar
“Ina ganin ba za a sake yi min wannan tambayar ba,” a cewarsa.
BBChausa.