Labarai

Yanda Wani Mutum Ke Daukar Hoton Matan Arewa Tsirara

Yanda Wani Mutum Ke Daukar Hoton Matan Arewa Tsirara

Wani lamari daya faru a Jos jihar Flato ya dauki hankulan jama’a inda aka bankado yanda wani mutum ya rika biyan matan Aure da ‘yan mata Naira Dubu 30 yana lalata dasu sannan kuma ya dauki hoton bidiyon abinda suke.

Abun ya fito filine bayan da aka saka hotunan bidiyon a wani shafin yanar gizo wanda kuma sanadin haka matan da aka gani a ciki suka fara fuskantar kyara da kuma abokansu na guje musu,kamar yanda Daily Trust ta ruwaito.

Mutumin me suna Emeka yana da kawaliya da yake biya Naira Dubu 10 akan kowace mace da ta kawo mai.

Rahoton ya bayyana cewa tuni daya daga cikin matan da aka gani a bidiyon ta hallaka kanta.

Emeka kan baiwa matan Dubu 30 ne nan take tare da alkawarin zai basu dubu 100. Ya kuma musu alkawarin cewa bazai saki bidiyon a Jihar ta Filato ko kuma cikin Najeriya inda yace a kasashen waje zai saki bidiyon.

Cikin wanda aka gano an yi wannan aika-aika dasu akwai kananan ‘yan mata da matan aure.

Tuni dai aka cire hoton bidiyon da aka dora a yanar gizo amma aikin gama ya gama dan da dama daga cikin matan da aka gani a bidiyon sun bar unguwanninsu saboda kyara.

A yanzu haka akwai kokarin da ake na ganin an dawo da wasu matan da aka yi wannan aika-aika dasu kan turba, kamar yanda wata Fasto, Jemimah Mbaya ta bayyana. Saidai tace tuni daya daga cikin ‘yan matan da ta fara tattaunawa dasu daya ta kashe kanta.

Hukumar ‘yansandan Flato ta bayyana cewa ta ji wannan rade-radi a gari amma babu wanda ya kai mata kara a hukumance inda ta yi kira ga wanda abun ya rutsa dasu da su zo koda a cikin sirri ne su kawo mata koke dan hukunta masu laifin.

Back to top button
error: Content is protected !!