Labarai

Yanda Wani Dan China Ya Hallaka Wata Budurwa

Innalillahi Wa’innaillahir Raji’un! Yanda Wani Dan China Ya Ma Budurwarsa Bahaushiya (Ummita) Yankan Rago A Garin Kano, Bisa Zargin Ta Yaudareshi.

Wani Labari Da Muke Samu, Marar Dadin Ji Shine Na Wani Dan Kasar China Mai Suna Mr Geng, Inda Yaje Har Gida Yayiwa Budurwarsa Ummita Yankan Rago A Unguwar Jan Bulo Dake Cikin Birnin Kano.

Shidai Mr Geng Sun Dade Tare Da Ummita Suna Soyayya, Inda Ya Kashe Mata Kudi Sosai, Ta Yanda Ita Marigayyar Har Kasuwanci Ta Fara Yi A Kasar Na China. Daga Baya Ne Kuma Ta Gudu Ta Barshi Inda Taje Tayi Aurenta.

Daga Baya Ne Kuma Auren Na Ummita Ya Mutu Inda Mr Geng Din Yaci Gaba Da Bibiyarta, Ita Kuma Taki Bashi Dama. Nan Ne Ya Fusata Inda Yaje Har Gida Ya Kwankwasa Kofa Mahaifiyar Nata Ta Bude Kofar, Inda Nan Ne Ya Sami Damar Caccakawa Ummita Wuka, Inda Wasu Ke Cewa Yankan Rago Ya Mata.

Daga Nan Ne A Karzaya Da Ummita Asibiti, Da Kaita Ba Jimawa Allah Ya Karba Rayuwarta, Shi Kuma Mr Geng Jami’an Tsaro Su Kamashi.

Ga Cikakken Labarin Yanda Lamarin Ya Faru.

 

NgHausa

I am YusHau Uba, CEO/Founder Of HausaMini.Com.Ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button