Labarai

Yanda Su Aure Juna Bayan Sun Hadu A Facebook

Yadda Wata Matashiya Tayi Wuf Da Saurayi Bayan Sun Haɗu A Facebook

Allah Ya yiwa wata matashiya gamdakatar yayin da tayi wuf da wani saurayi bayan da suka haɗu a kafar sada zumunta ta facebook inda daga bisani suka yi aure bayan an shafa fatiha aka kuma sha buki.

 

Matashiyar mai suna Fatima tayi wuf da angonata ne, wani lokaci bayan suna cikin chat a facebook sai ya ce mata za shi masallaci, sai ta ce masa don Allah yayi mata addu’a domin babban burinta shi ne Allah ya bata mijin aure mai nagarta, nan take angon nata ya ce, “ko nayi maki?” Nan ta kaɗa baki ta ce ƙwarai kuwa, kamar da wasa, sai angon yace to ai shi ke nan, na sami mata, haka kuma aka yi, su kayi aure ba da jimawa ba.

Angon ne ya bada wannan labarin inda ya sanya hotonsa da na Amaryarsa tare da hirar tasu a lokacin, kamar yadda kuke gani a kasa.

Kuma zaku iya kulla alakar Aure a Facebook?

Back to top button
error: Content is protected !!