Kannywood

Yanda Nake Hada Fim Da Siyasa – Rukayya Dawayya

Rukayya Umar Santa, wacce aka fi sani da Dawayya, tsohuwar jaruma ce kuma furodusa a masana’antar Kannywood. A hirar da jarumar tayi da Weekend Magazine, ta bayyana yadda ta tsunduma harkar siyasa da sauransu.

Kamar yadda jarumar ta bayyana, ta dawo Kano ne a lokacin da take da shekaru 15 a duniya. Ta kuma so fara shirin wasan kwaikwayo, amma an bata shawarar dakatawa har ta kara girma.

Bayan kammala sakandire ne ta fada harkar fim din inda ta fara da fim mai suna ‘Dawayya’, wanda daga nan ne ta samu sunan ya bi ta. Ta bayyana cewa ta yi difuloma inda daga baya ta koma BUK. Ta bayyana cewa, tana goyon bayan karatun ‘ya’ya mata dari bisa dari.

A halin yanzu tana koyarwa a wata makarantar Islamiyya.

A lokacin da jaridar Daily Trust ta tambaya jarumar yadda ta fada harkar siyasa, sai ta ce: “Saboda na kasance ‘yar wasan kwaikwayo, fadawa siyasa bata yi min wuya ba. Dama can nayi suna kamar dai yadda aka san ‘yan fim nayi.

Hakazalika, siyasa ta kara fadada min iya mu’amala da mutane da kuma kungiyoyi.” “Nayi kamfen na zaben Shugaan kasa Muhammadu Buhari kuma ya ci. Nayi wa gwamnan Kano da Katsina kuma duk sun yi nasara.

A don haka zan ce, nayi nasara a kamfen din siyasa da nakeyi.” In ji jarumar. A lokacin da aka tambayi jarumar dalilin da yasa ta fada harkar siyasa, sai ta ce, “Siyasa a gaskiya ta zama min tamkar karin ilimi kuma mabudin ido.

Masana’antar fim ta banbanta da siyasa. Siyasa ta kara min karfin guiwa da kuma fatan sauya kasar nan. Ta kara min tunani fiye da masana’antar fim din.

Na fara tunanin sauya rayuwar mutane. Ina ganin zan iya fitowa takara kuma ina ji a jikina zan ci.” A cewarta.

Back to top button
error: Content is protected !!