Yanda Mu Shafe Shekaru 8 Muna Soyayya Daga Baya Ya Aure Wata
Budurwa Ta Bayyana Yanda Su Shafe Shekaru 8 Suna Soyayya Da Saurayinta Daga Baya Yaki Aurenta Ya Zaga Ya Aure Wata.
Maryam Nuruddeen Shuwa Gwammaja ta bayyana yadda Saurayinta ya yi mata Yankan Kauna bayan shafe shekaru 8 suna Soyayya.
Ta ce ya rika bata kudi tana siyo kayan lefe ashe wata take hadawa sai saura kwana daya aurensa ta gano abin da ya dangana da ita zuwa gadon Asibiti.
Maryam nuradeen shuwa ta fara bada wannan labarin a kafar sadarwa ta titkok inda wannan labarin yayi matuƙar tayar da kura a kafaffen sada zumunta.
Gidan rediyon Dala fm kano sun samu zantawa da yarinyar inda ta basu labarin yadda soyayyar su ta fara har i zuwa lokacin kacin da yayi kan mage ya waye yayi wuff da wata ya barta da gadon asibiti.
Maryam yar shuwa tana cewa :
“Daga wasa soyayya ta fara amma daga baya ta lalace, na fara son shi ne ta dalilin wata yar uwarsa wanda takai kala bana kula shi har ina kula shi muna soyayya sosai mun shaku mun dauki tsawon shekara 8 muna soyayya.
“Muna muna soyayya sai maganar aure ta shiga gidan su an sami nema gidan mu an sani”
To Fa a nan ne mai gabatar da shirin ya tambayeta sai minene ya faru?
Maryam shuwa ta kara da cewa:
“Kawai ina zaune da dare kamar wasa na duna status din wani abokinsa sai naga katin daurin aurensa a status sai na kalla sai na sake kalla sai naje nayiwa abokin nasa magana sai abokin nasa yace eh bai gayamiki ba, ae gobe ne daurin aure sai nace daurin aure gobe sai yace eh.
Kuma a ranar da naga status nashi munyi Waya da shi yarda yayata sunyi waya kuma duka maganar akan maganar bikina da ni da shi abinda ya faru kenan sai kawai nayi “sccreen shot” sai na tura mishi sai ya kirani inji ta”
Sai yace min wai ina naga wannan abu nace a’a kamar ya ina gani me hakan yake nufi saboda ni farko ganin abun nake kamar wasa , kamar wani fim ake haska mu, ko a mafarki nake gani.
Sai yace min eh waye ya gayamin sai tace kamar kai ne ko ba kai bane yacemin eh shine amma dan Allah na tsaya na fahimce shi.
To fah a nan ne zakuji babban labari ku saurare ta hanyar wannan bidiyo domin hausawa kance waka a bakin mai ira tafi dadi.
Daga: HausaLoaded