Yanda Matashi Ya Sace Budurwa Har Tsawon Shekaru 7
ABIN MAMAKI: A Garin Zaria An Kama Wani Da Ya Boye Wata Budurwa Na Tsawon Shekaru Bakwai Har Sai Da Ta Haifa Masa Yara Uku
Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Sabon Gari Zaria ta samu nasarar ceto wata budurwa mai suna Rabi’ah Salisu ƴar kimanin shekaru 22 da wani saurayi mai suna Joe Abdulmumin ɗan kimanin shekaru 30 ya ɓoye ta kimanin shekaru bakwai da suka wuce a gidan su dake unguwar Dogarawa a karamar Hukumar sabon Gari, kuma har ta haifa masa yara guda uku (biyu mata ɗaya namiji).
Dubun sa ya cika a jiya Alhamis 28/12/2023.
A hirar da majiyarmu ta yi da mahaifinsa wanda yake makaho ne ya shaida cewa ya yi ya yi ɗan nasa ya mayar da yarinyar amma abin ya fi karfin sa.
Mahaifin ya shaidacewa asalinsa ɗan garin Madobi ne dake Jihar Kano amma kuma shi ba musulmi bane ķìŕìśťà ne.
A yayin hira da yayan Rabi’ah Malam Abdullahi Salisu ya ce shekaru bakwai kenan suna neman ƙanwarta su da ta baro gida daga gidan su a unguwar Jaba daga nan basu ƙara jin ɗuriyar ta ba sun yi addu’a daga baya suka mayar da komai ga Allah.
Tuni dai aka mika shi ga Jimi’an tsaron ƴan sanda domin cigaba da bincike da kuma gurfanar da shi gaban ƙulliya domin ya girbi sakamakon wannan mummunan aikin da ya aika ta.