Yanda Matashi Ya Hallaka Ladani A Garin Kano
Yanda Wani Matashi A Kano Ya Hàĺĺàķa Ladanin Masallaci Sakamakon Hana Su Shaye-shaye Da Ya Yi
Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano
Lamarin dai ya faru ne a daren Ranar Lahadi 31 ga Watan Disamba an shaidi matashin Ladanin mai suna Muhammadu Sani (Baha) a matsayin mutumin kirki, kuma shine ma ya ja sallar magriba a masallacin da yake ladanci a kasuwar Kurmi ‘yan kaji.
Jiya ya gamu da ajalin sa, sakamakon kisan gilla da wannan matashi ya yi masa.
Abin da ya faru shine a kwanakin baya shi wannan yaron suna shaye-shaye a kofar gidan marigayin sai ya yi musu magana cewa “su daina yi musu shaye-shaye a wurin” ashe shi yaron ya ƙullaci Ladanin, shine jiya bayan marigayin ya ja sallar Magriba an idar, sai ya ɗauki robobin ruwa guda biyu da ya ɗebo a famfo zai kai gidan sa, ashe makashin yana laɓe a kofar gidan da wùķa a hannun sa, yana ƙarasowa ɗauke da jarkokin ruwa kawai sai yaron ya zaro wùķà ya caka masa, kafin jama’a su ankara ya gudu.
Nan Muhammad Sani, ya shiga gida yana dafe cikin, jini yana ɗibar sa, kafin wani lokaci Allah ya karɓi ransa.
Anyi jana’izar sa kamar yadda addinin muslumci ya tanadar.
Muna roƙon Allah Ya gafartawa Muhammadu Sani, Ya sada shi da Annabi Muhammadu SAW.
Cikin Ikon Allah A Ranar Talata Jami’an Tsaro Sunyi Nasarar Cafko Wannan Matsashin Da Yayi Wannnan Aika Aikan. Inda Yanzun Haka Yana Hannun Jami’an Tsaro,