Yanda Ginin Rufin Masallaci Ya Ruftowa Wasu Bayin Allah Ana Tsaka Da Sallah A Babban Masallacin Zaria
Innalillahi Wa’inna Illaihir Raji’un! Yanda Ginin Rufin Masallaci Ya Ruftowa Wasu Bayin Allah Ana Tsaka Da Sallah A Babban Masallacin Zaria.
A Ranar Jumma’a, 24 ga watan Al-Muharram, 1445 AH kuma 11 ga watan Agusta, 2023. Allah tabaraka wata’ala Ya yiwa ‘yan uwanmu rasuwa a sakamakon ruftawar rufin kwanon Babban Masallacin Jumma’a na Kofar Fadar Mai Martaba, Sarkin Zazzau.
Wannan ibtila’i ya faru ne a daidai lokacin da ake gabatar da La’asar a cikin Masallacin. A karkashin jagorancin Ratibin Masallacin Jumma’a na Zazzau. Duk yadda za a bayyana yadda al’amarin ya faru, tausayi da jimami ba zasu bari ba. Saboda haka Allah Ya kaddara haka ta faru ga wadannan ‘yan uwan namu. Kuma mun karba da zuciyar imani.
Duk da saukar ruwan sama da ake yi a Zaria a lokacin da za a gabatar da Sallar Jana’izar.
Mai Martaba, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR tare da manyan ‘yan Majalisar Sarki, Hakimai, Dagatai, Masu Anguwanni, dangi, Shugabannin al’umma, kungiyoyin al’umma dabam-daban ‘yan uwa da sauran jama’a, Allah Ya bamu ikon halartar Sallar jana’izar mutane takwas din da suka rigamu Gidan gaskiya. Allah Ya jikansu da rahama.
Muna yiwa wadanda suka sami mummunan rauni a sakamon wannan ibtila’i addu’a. Allah Madaukakin Sarki Ya basu lafiya. Allah Ya sa kaffara ce a gare su. Allah Ya kare aukuwar irin haka nan gaba a ko ina. Allah Ya tsare mana imaninmu da mutuncinmu da lafiyarmu da kuma rayuwarmu a duk inda muke.
Muna mika sakon gaisuwar ta’aziyya ga Mai Martaba Sarkin Zazzau da kuma dukkan dangin wadannan bayin Allah. Allah Ya karbi shahadarsu, Ya sa mutuwa hutu ce a gare su kuma Allah Ya sa ruhunsu yana cikin Gidan Aljanna Firdausi,
Allah Ya bamu dacewa da cikawa da imani in lokacinmu ya yi. Allah Ya jikanmu da rahama, Ya gafarta mana dukkan zunubanmu, Aamin.
Wasu Daga Cikin Mutanen Da Su Tarar Da Ajalinsu Yayin Ruftawar Ginin Masallacin

Yau Husaini Hussain Zakariyya
Ya Bishi
Ubangiji Allah Ya Gafarta Muku Yasa Aljanna Tazama Makoma Agareku
Jinyar Da Kukayi Allah Yasa Tazama Kaffara Agareku Ameen

Sunan shi Nuradeen Haruna (haske) yana Ganganfa ( fan wanki) Cikin garin Zariya.
Yana cikin wanda gininin masallacin juma’a Zariya ya ruftawa , yarasu anyi Jana’izar su.
Allah yajikanshi yasa aljanna makoma
Allah yayiwa Mal. Abubakar (Mal. Garba) rasuwa sakamakon ruftawan rufin ginin masallacin fada ayau jumma’a. Marigayin mahaifine ga Hon. Barr. Bashir Abubakar dan majalisa mai wakiltan bukuyyum ta arewa jihar Zamfara.