Bidiyo
Yanda Auren Jaruma Maryam Malika Ya mutu, Bayan Shekaru A Gidan Miji
Ana kishin-kishin din auren tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Malika ya mutu bayan shekaru A Dakin Miji.
Rahoton hakan ya fitone daga Kannywood exclusive kamar yanda suka wallafa a shafinsu na YouTube tun a shekarar data gabatane aka rika rade-radin mutuwar auren jarumar bayan da aka rika ganinta a Kaduna.
Rahotan ya bayyana cewa da wakilan majiyarmu suka yi yunkurin jin ta bakinta, Jarumar bata musu wani cikakken bayani ba. wani na kusa da jarumar ya tabbatar da cewa auren nata ya mutu.
Ya kara da cewa bata son yin maganane saboda kada ta nuna ta damu da mijin nata. Tana jira shi ya fara magana kamin ta mayar masa. Maryam Malika kanwace ga marigayiya, Balarana, tsohuwar matar Sha’aibu Lawal Kumurci.