Kannywood

Yanda Aka Saki Bidiyon Tsaraicin Maryam Booth

Shugabannin masana’antar finafinan Hausa su na taimaka wa jami’an tsaro domin kama wasu mutum biyu da ake zargi da ɗaukar wani hoton bidiyo tsaraicin Maryam Booth tare da yaɗa shi a soshiyal midiya.

Tun daga jiya ne guntun bidiyon ya ɓulla ya fara yawo gadan-gadan a gari.

An faɗa wa mujallar Fim cewa yau shekara uku kenan da ɗaukar bidiyon.

A bidiyon mai tsawon daƙiƙa 2 kacal, an ga kyakkyawar jarumar ta Kannywood tsirara timɓir a cikin ɗaki kamar ta fito daga wanka babu komai a jikin ta sai ɗankwali a kan ta.

Akwai tabbacin cewa wanda ya yi bidiyon ya ɗauke ta ne da gangan, ba tare da amincewar ta ba, domin kuwa da ta ankara ana ɗaukar ta sai ta yi wuf ta ƙwace wayar da ake ɗaukar ta da ita.

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jarumar, amma wakilin mu ya ji wayar ta a kashe.

Sai dai shugaban ƙungiyar jaruman Kannywood ta Jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, ya tabbatar wa da mujallar Fim cewa ƙungiyar sa ta shiga cikin al’amarin, ta na taimakawa wajen ƙoƙarin kamo wasu mutum biyu, namiji da mace, waɗanda aka tabbatar da cewa su ne su ka saki bidiyon a gari bayan sun jima su na cutar Maryam tare da yi mata barazana.

A cewar Kwalle, a tsawon shekaru uku da su ka gabata matasan biyu sun dinga karɓar kuɗi a hannun jarumar a bisa tsoratarwar cewa idan ta hana su kuɗin za su saki bidiyon duniya ta gani.

Kwalle ya ce, “To gaskiya wannan abu ne da ya shafi rayuwar ta, ba na harkar fim ba ne.

“Amma abin da mu ka bincika mu ka samu labari shi ne wannan abin ya faru ne kusan shekaru uku da su ka wuce.

“Kuma yaran da su ka yi abin sun yi ta yi mata barazana da shi, kan ta ba su kuɗi, idan ba haka ba za su saki bidiyo ɗin, kuma a kan haka sun karɓi kuɗi masu yawan gaske a wajen ta don gudun kada abin ya bayyana.

To a shekaranjiya Laraba ne ɗaya daga cikin su ya ce ta ba shi kuɗi zai kai mahaifiyar sa asibiti, ita kuma ta ce ba ta da kuɗi kuma ta gaji da ba su kuɗin.

“Don haka ganin ba su samu kuɗin ba su ka saki bidiyo ɗin.

“Kuma akwai shaida ta banki yadda ta rinƙa tura masu duk abin da su ka nema a wajen ta, don haka ana nan yanzu ana bin hanyar da za a kama su.”

Shi kuwa sakataren ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta ƙasa (MOPPAN), reshen Jihar Kano, Malam Salisu Muhammad Officer, da mujallar Fim ta yi masa tambaya dangane da lamarin, sai ya ce, “Mun san da maganar, amma mu a matsayin mu na shugabannin harkar fim babu wani abu da za mu ce. Kawai abu ne da ya shafe ta, ba harkar fim ba.”

A yanzu dai waɗanda ake zargi da sakin bidiyon sun yi ɓatan dabo, jami’an tsaro na neman su ruwa a jallo.

Wata ƙawar Maryam Booth ta faɗa wa mujallar Fim cewa al’amarin ya girgiza jarumar matuƙa, har ta yi ta kuka domin baƙin ciki “kan wannan cin amana da aka yi mata.”

Wakilin mu ya samu labarin cewa yawancin ‘yan fim da su ka ji labarin ɓullar bidiyon sun tausaya wa Maryam, su na faɗin cewa ba laifin ta ba ne, kuma ba sabon abu ba ne yarinya ta fito daga wanka a banɗaki tsirara a gaban ƙawar ta, musamman a cikin ɗaki.

Wakilin mu ya ruwaito cewa ba kasafai ake samun irin abu ya shafi ‘yan fim ba.

Ya ce rabon da wani bidiyon tsiraici na wani ɗan fim ɗin Hausa ya ɓulla a soshiyal bidiya tun shekarar da bidiyon Maryam Hiyana ya fita.

A fagen siyasar Nijeriya kuwa an sha samun bidiyoyin tsiraici na zaɓaɓɓun shugabanni da waɗanda aka naɗa muƙamai sun ɓulla a soshiyal midiya.

Ko a farkon wannan makon wani guntun bidiyo ya ɓulla a kafafen sada zumunta na wani sanata daga arewacin ƙasar nan, shi ma ya fito zigidir daga ɗakin wanka.

Mujallar film

Back to top button
error: Content is protected !!