Labarai

Yanda A Sace Ragon Layya Na Limami A Garin Jos

Yadda Aka Sace Ragon Liman A Jos

An sace ragon babban limamin unguwar Ali da ke karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, Imam Abdulkadir.

An sace ragon ne a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar jajibirin idin sallah babba

Malam Haruna Yaqub, Limamin Al’umma ne a yankin , wanda ya bayyana hakan a lokacin huɗubar da ya gabatar jim kadan bayan kammala Sallar Raka’a biyu na idi, inda ya yi Allah wadai da lamarin, ya kuma bayyana lamarin a matsayin mara daɗi.

“Ragon Babban Limaminmu, wanda ya siya ya yanka, an sace shi cikin dare, mun yi matukar kaduwa da lamarin, mun yi mamakin jin wannan labari, wannan yana nufin mutane ba sa tsoron Allah, kuma abin ban tsoro ne yadda mutane suka kai ga satar ragon da ake nufi da ayyukan addini,” inji Yaqub.

Yaqub, ya kuma yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah, kuma kada su yi sata, ko kuma su aikata wani laifi, yana mai jaddada cewa kowa zai yi bayani kan duk abin da ya aikata a nan duniya a lahira.

Ya ce: “Lokaci ya yi da mutane za su tuba kuma su ɗauki tafarkin Allahkuma na a makara ba, don haka ya kamata mutane su daina aikata munanan abubuwa kuma su yi aiki da dokokin Allah.”

Back to top button
error: Content is protected !!